An kashe akalla mutane hudu a Sokkoto

Najeriya
Image caption Tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya

Mutane akalla hudu ne ake zargin sojoji sun harbe har lahira a wani gida da ke unguwar Gidan -Igwai da ke Sokoto a arewacin Najeriya .

Wannan al'amarin dai ya faru ne da yammacin ranar juma'a.

Wani mazaunin wurin da ya ganewa idonsa lamarin, ya shaidawa BBC cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe biyar na yammacin ranar Juma'a, inda ya yi zargin cewa sojoji ne da dama da suka isa unguwar a motocin su, suka nufi wani gida, sannan suka budewa gidan wuta.

Ganau din ya ce an kashe mutane uku a cikin gidan, sannan ya yi zargin sojojin da fito da mutum guda kuma, shima suka harbe shi.

Mutanen da aka kashe dai baki ne a unguwar wanda ba su fi shekara guda da zuwa ba, kuma 'yan kasuwa ne inji shi.

BBC ta tuntubi mai magana da yawun sojojin Birget ta daya na jahohin Sokoto da Kebbi da Zamfara , kuma ya shaidawa wakilin mu Abdou Halilou cewa yana kan bincike domin samun bayanai.