Amurka ta yi Allawadai da boma-boman Iraqi

harin bam a Bagadaza
Image caption harin bam a Bagadaza

Amurka ta yi Alawadai da harin da aka kai a Iraqi, inda wasu jerin bama-bamai da harbe-harbe suka kashe mutane fiye da sittin a lokacin da ake bukukuwan kammala azumin Ramadan.

Bama baman sun tashi ne a yankunan 'yan Shi'a na Baghdad inda mutane fiye da sittin aka bada rahotan cewa sun hallaka, wasu kuma suka samu raunuka.

'Yan sanda sunce an nufi kasuwanni ne inda mutane ke yin hada hada da kantinan saida shayi dana abinci.

An dai tsaurara matakan tsaro a makon daya gabata domin kare mutane a lokacin bukukuwan da ake yi a karshen watan azumin Ramadan.

Watan ramadanan wannan shekarar dai shine mafi tashin hankali da aka gani tun shekarar 2007 inda aka kashe fiye da mutane dari shida da saba'in.

Mafiywancin tashe tashen hankulan da aka gani a watanni shidan da suka gabata dai sun hadar da mayaka masu kaifin kishin Islama ne na 'yan Sunni dake kai hari lardunan 'yan Shi'a.