Palasdinawa sun la'anci gine-ginen Isra'ila a yankunansu

Gine- ginen Isra'ila a yankunan Palasdinawa
Image caption Gine- ginen Isra'ila a yankunan Palasdinawa

Wakilan Palasdinawa a shawarwarin sulhu sun zargi Isra'ila da kokarin yin kafar angulu a tattaunawar da za a yi cikin mako mai kamawa, bayan sanarwar da ta bayar na gina karin matsugunan Yahudawa a yankunan da ta mamaye.

Mai fafutukar 'yancin Falasdinawa, Hanan Ashrawi, ta sheda wa BBC cewa babu dalilin tattaunawa idan Isra'ila ba a shirye take ta sauya manufofinta ba.

Ministan gidaje, Uri Ariel, ya ce za a gina su ne a Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma gabacin birnin Kudus.

An yi sanarwar ce kwanaki uku kafin sake ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a birnin Kudus