An kammala zabe zagaye na biyu a Mali

Zabe a Mali
Image caption Zabe a Mali

A Mali an rufe runfuna a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka yi a yau, Lahadi.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kawo cikas ga zaben, abin da ya sa masu sa ido suka yi hasashen fitowar jama'a ba za ta kai ta zagayen farko ba.

Wani mai nazarin siyasa a Malin, Demba Boundy, ya yaba da tarin mutanen da suka fito kada kuri'unsu a karon na farko, yana cewa yanzu karin Maliyawa sun amince, ko sun fahim cewa kuri'arsu tana yin tasiri ko za ta iya yin tasiri. Ana fafatawa ne tsakanin 'yan takara biyu da suka fi samun kuri'u a zagayen farko, tsohon firaminista, Ibrahim Boubakar Keita da kuma Soumaila Cisse, tsohon ministansa na kudi.

Karin bayani