Zaben Shugaban Kasa a Mali

Zabe a Mali
Image caption Daruruwan masu sa ido akan zabe ne zasu shaida zaben

Al'ummar Kasar Mali zasu kada kuri'arsu yau a zagaye na biyu na zaben Shugaban Kasa a yau.

'Yan Mali zasu zabi tsakanin Ibrahim Boubacar Keita, wanda ya samu kuri'u sama da kashi 39 cikin 100 a zagayen farko da Kuma Soumaila Cisse wanda ya samu kuri'u sama da kashi sha tara 19 cikin 100.

Ibrahim Boubacar Keita wanda aka fi sani da IBK ya bukaci masu kada kuri'a a Mali da su bashi abinda ya kira wani kyakyawan rinjaye a zagaye na biyu na zaben.

Yace abu na farko da zai baiwa mahimmanci a matsayin Shugaban Kasa shine sasantawar Kasar.

Amma ya kuma ce zai nemi zaman lafiya na hakika bana karya ba.

Yana kuma da goyan bayan shugabannin masu sassaucin ra'ayin Islama masu karfin fada aji.

Abokin hamayyarsa a zagaye na biyu na zaben shine Soumaila Cisse wani tsohon ministan kudi, wanda ya dau alkawarin inganta ilimi da samar da ayyuka da kuma yiwa rundunar sojin Kasar garanbawul.

Soumaila dai yafi fitowa karara yana sukar shugabannin da suka jagoranci juyin mulkin sojin kasar a bara fiye da Mr Keita.

Karin bayani