Boko Haram ta dauki alhakin kai hare-hare

Imam Abubakar Shekau
Image caption Shugaban Kungiyar Boko Haram

Kungiyar Jama'atu Ahlis Sunah lid Da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta ce ita ce ta kai wasu jerin hare-hare a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Kungiyar ta dauki alhakin kai hare-haren ne a wani hoton bidiyo na baya-bayan nan da ta fitar.

Shugaban kungiyar, Imam Abubakar Shekau, ya jaddada cewar yana nan cikin koshin lafiya.

Shugaban kungiyar ya ce hare haren sun hada da wadanda aka kai Malam Fatori da Bama, inda jami'an sojoji a kwanakin baya suka ce an hallaka mutane 35

Haka kuma ya ambato hare haren da aka kai zuwa garuruwan Baga da Gamboru Ngala da ke iyaka da kasar Cameroon.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a jihohi ukku da suka hada da Borno domin yaki da 'yan kungiyar.