Cin zarafin kananan yara a China

Image caption Yara 'yan makaranta a China

Gidajen watsa labarai na kasar China sun buga labarai kan yadda ake cin zarafin yara 'yan makaranta, musamman 'ya'yan ma'aikata 'yan ci-rani a kasar.

Akasari wannan lamari kan afku ne a yankunan karkara, idan iyayen yaran sun tafi wuraren ayyukansu.

A ranar 8 ga watan Agusta, 'yan sanda sun tsare wani mutum mai shekaru 62 a birnin Ruichang, da ke lardin Jiangxi, saboda ya yi lalata da wata yarinya 'yar shekaru bakwai a duniya.

'Abin tayar da hankali'

Mutumin, wanda ya koyar a wata makaranta da ke yankin mai cike da tsaunuka tsakanin watan Satumba na shekarar 2012 zuwa watan Mayu na shekarar 2013, ya yi lalata da dalibansa guda bakwai wadanda ke da shekaru tsakanin takwas zuwa tara a bayan ajinsu, inda ya yi ikirarin cewa yana duba ayyukan da suka yi ne.

Hakan dai ya sanya yaran sun kamu da cututtuka masu nasaba da jima'i.

Kafafen watsa labaran kasar sun ce dukkan iyayen yaran 'yan ci-rani ne.

Image caption Iyaye ma'aikata

Mutumin ya amince da aikata wannan laifi, kuma 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike a kan batun.

'Ruwan dare'

Wannan lamari na faru ne kwanaki kadan bayan an kama wani malami a lardin Shanxi game da zargin yin lalata da kananan yara 'yan makaranta da dama.

Masu sharhi na ganin cewa wannan batu kadan ne daga cikin dubban rahotanni na yin lalata da kananan yara da ke faruwa a kasar.

A watan Mayu kawai, an samu rahotannin yin lalata da kananan yara 'yan makaranta guda takwas cikin kwanaki ashirin, lamarin da ya tayarwa da iyaye hankali kana ya jawo zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta da jaridun kasar.

Karin bayani