Cin hancin sayar da magunguna a China

Kamfanin sarrafa magunguna na GlaxoSmithKline
Image caption Kamfanin GlaxoSmithKline na fuskantar bincike a China

Wani ma'aikacin kamfanin magunguna a China ya ce kusan koda yaushe suna bayar da cin hanci domin kara yawan magungunan da suke sayarwa.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC.

Wani ma'aikacin ya ce kamfaninsa ya biya kusan dala dubu daya domin wani asibiti ya koma yin amfani da magungunansa.

Wakilin BBC a Beijing ya ce hukumomi a kasar na fadada bincike a kan kamfanonin sarrafa magunguna na kasashen waje.

Lamarin ya biyo bayan zargin da aka yi wa kamfanin Birtaniya, GlaxoSmithKline na aikata munanan laifuka.