China na gaban Amurka a Afrika —Clinton

Image caption Bill Clinton da 'yarsa Chelsea a nahiyar Afrika

Tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton, ya amince cewa kasarsa tana bayan China wajen zuba jari a nahiyar Afrika.

A wata hira da ya yi da BBC, Mista Clinton ya ce a bangaren lafiya ne kawai kasar Amurka ta fi China tallafawa kasashen Afrika.

A cewarsa, Amurka ba ta kashe kudin a-zo-a-gani ba a ayyukan samar da ababen inganta rayuwar jama'a da kuma fannin bunkasa tattalin arziki.

Sai dai kuma ya ce, abu ne da zai iya yiwuwa a samu hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu domin aiki tare a nahiyar Afrika, maimakon a ce daya ce ta kankane harkokin ci gaban nahiyar.

Karin bayani