Sojan Faransa ya shirya hari kan Masallaci

Birnin Pari na Faransa
Image caption Akwai miliyoyin Musulmi a Faransa

An cafke wani sojan Faransa bisa zarginsa da shirin kai hari kan wani masallaci, inji ma'aikatar cikin gida ta kasar.

Sojan mai shekaru 23 ya taba kai hari kan wani masallaci kuma yana da ra'ayin rikau.

Wata sanarwa ta ce ma'aikatar leken asiri ta kasar ta yi wa sojan tambayoyi, kuma tana tuhumarsa da laifin mallakar makamai domin aikata ayyukan ta'addanci.

Wata majiya ta bayyana wa kamfanin dillacin labarai cewa, sojan ya yi niyyar kai hari ne a wajen garin Lyon, a dai dai lokacin da Musulmi ke kammala azumin watan Ramadana.