Palasdinawa 26 za su samu 'yanci

fursunan palasdinawa
Image caption Za a saki fursunonin ranar Talata

Gwamnatin Isra'ila ta amince da sakin fursunonin Palasdinawa su ashirin da shida a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da za ta sa a sake komawa kan tattaunawar shirin zaman lafiya a makon gobe.

Za dai a saki fursunonin ranar talata.

Sanarwar na zuwa ne bayan da jami'an diplomasiya suka zargi Isra'ila da kokarin yin zagwon kasa ga tattaunawar zaman lafiya ta hanyar amincewa da gina sabbin gidaje har guda kusan 1,200.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila ya yi watsi da sukar da ake yi ,yana mai cewa duk wani shirin zaman lafiya ya zuwa yanzu, ya nemi matsugunan da ake magana akansu yanzu su kasance karkashin yanki na Isra'ila kuma Palasdinawa a shirye suke su amince da musayar filaye.

Karin bayani