'Gine-ginen Isra'ila ba za su kawo cikas ba'

John Kerry
Image caption Isra'ila zata gina karin gidaje a yankunan da Palasdinawa ke ikirari

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce sanarwar da Isra'ila ta yi na gina sabbin gidajen Yahudawa zai kawo cikas ba.

Mr. Kerry ya ce gidajen na 'yan kama wuri zauna ba zai kawo cikas ga tattaunawar zaman lafiyar da za a dawo da ita a wannan makon ba.

Mr. Kerry ya ce daman ana tsammanin Isra'ilan za ta yi wannan sanarwa, Kuma Amurka na kallon gina dukkanin matsugunnan Yahudawan, a matsayin abin da ya sabawa doka.

A ranar Lahadi ministan gidajen Isra'ila ya amince da shirye shiryen gina sabbin matsugunai fiye da dubu daya a gabar yamma da kogin jordan da kuma gabashin birnin Qudus, yankunan da Palsdinawa suke cewa nasu ne.

Karin bayani