An kashe mutane kusan 50 a Masallaci

Hari a Najeriya
Image caption Jihar Borno tana fama da rikicin Boko Haram

Wata majiya mai karfi ta shaidawa BBC cewa 'yan bindiga 200 sun kai hari a wani masallaci dake garin Konduga a lokacin sallar asuba, inda suka kashe mutane kusan hamsin.

Akwai yiwuwar 'yan bindigar da suka kai harin, sun yi hakan ne saboda tunanin cewa wasu daga cikin 'yan sintirin na yin sallah a cikin masallacin.

A baya dai kungiyar nan ta Jama'atu Ahlussunna liddawa'ati wal jahad da aka fi sani da Boko Haram ta sha kaddamar da hare-hare a yankin a kan majami'u, a wasu lokuta ma a kan masallatai.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci dai a yankin arewa maso-gabashin Najeriya kusan watanni uku da suka wuce.

Gwamnatin Borno

Mai magana da yawun gwamnatin jahar Borno, Malam Isa Umar Gusau ya shaidawa BBC cewa hare-haren sun tadawa gwamnan jahar hankali.

Abin da ya sa gwamnan ya kira wani taron gaggawa a ranar Talata tare da jami'an tsaro.

"Zai kuma kai ziyara garin Konduga domin ganawa da iyalan wadanda lamarin ya shafa" In ji Malam Isa Umar Gusau.

Gwamnatin Jahar Borno ta kuma yi kira da a ci gaba da addu'oi, ta kuma ce za ta ci gaba da iyakacin kokarinta wajen inganta tsaro a Jahar.

Boko Haram

Kungiyar Jama'atu Ahlis Sunah lid Da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta ce ita ce ta kai wasu jerin hare-hare a Jihar Borno.

Kungiyar ta dauki alhakin kai hare-haren ne a wani hoton bidiyo na baya-bayan nan da ta fitar.

Shugaban kungiyar, Imam Abubakar Shekau, ya jaddada cewa yana nan cikin koshin lafiya.

Shugaban kungiyar ya ce hare-haren sun hada da wadanda aka kai Malam Fatori da Bama, inda jami'an sojoji a kwanakin baya suka ce an hallaka mutane 35.

Haka kuma ya ambato hare-haren da aka kai zuwa garuruwan Baga da Gamboru Ngala da ke iyaka da kasar Kamaru.