Dole ne magoya bayan Morsi su koma gida

Image caption Magoya bayan Morsi

Ministan harkokin wajen kasar Masar Nabil Fahmy, ya shaidawa BBC cewar dole ne sai magoya bayan hambararren Shugaban Masar, Mohammed Morsi sun kawo karshen zaman dirshan din da suke yi saboda tsaikon da suke jawowa.

Mista Fahmy ya ce gwamnati na saran shawo kan matsalar ta hanyar tattaunawa, amma idan har sai 'yan sanda sun dauki mataki a bisa tsarin doka, tabbas za suyi hakan don kawar da masu zanga-zanga.

Da farko, rahotanni sun nuna cewar daga yau (Litinin) hukumomin Masar za su fara aikin kawar da sansanonin da aka kafa.

Dubban masu zanga-zanga ne suke yin kiran a maidoda Mista Morsi a kan mulki.

A cewar Mista Fahmy, gwamnatin Masar za ta ci gaba da tattaunawa da magoya bayan Morsi don gina makomar kasar.

Karin bayani