An rufe masallaci a Sri Lanka

Image caption Masallacin da aka rufe a Colombo

An rufe wani masallaci a babban birnin kasar Sri Lanka bayan da gungun mabiya addinin Budda sun kai masa hari, lamarin da ya janyo rikici har mutane biyar suka samu raunuka.

Musulmi a yankin Grandpass da ke Colombo za su ci gaba da mallakar tsohon masallacinsu da ke kusa, wanda a da ake shirin rushewa saboda da ayyukan cigaban birnin.

An yi Alla-wadai da matakin gwamnati na kasa tsare wadanda suka kai harin.

A 'yan watannin nan, gungun masu tsattsauran ra'ayin addinnin Budda sun kaddamar da hari a kan Musulmai da Kiristoci.

A lokacin Sallah Isha'i daren Asabar, wasu gungun 'yan Budda sun jefa duwatsu a cikin masallacin, abin da ya janyo kafa dokar-hana-fita wacce daga bisani aka sassauta.

Karin bayani