'Yara dubu 100 na fuskantar lalata'

Tambarin kungiyar agaji ta Save the children
Image caption Tambarin kungiyar agaji ta Save the children

Kungiyar agaji ta Save the Children ta yi gargadin cewa, kananan yara fiye da dubu 100 na fuskantar barazanar yin lalata da su a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Ko kuma tilasta musu shiga kungiyoyi masu dauke da makamai, a cewarta.

Kungiyar ta ce, an tilasta wa yaran barin muhallinsu, bayan 'yan tayawe sun kawar da gwamnatin shugaba Bozize, a watan Maris din da ya wuce.

Inda ta kara da cewa da yawa daga cikin yaran na fama da yunwa da kuma zazzabin cizon sauro.

A ranar Laraba kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna a kan halin da jamhuriyar Afrika ta tsakiyar ke ciki.