An yankewa mutane 2 hukuncin kisa a China

Image caption Shugaba Xi Jingping

Wata kotu a kasar China ta yankewa mutane biyu hukuncin kisa saboda shiga cikin kungiyar 'yan ta'adda wacce ta kaddamar da hari a lardin Xinjiang dake yammacin kasar.

Harin ya janyo sanadiyyar mutuwar mutane akalla ashirin da daya.

Kafafen yada labarai a kasar China sun ce a yankewa wasu mutane uku hukuncin dauri mai tsawo a gidan kaso.

Rikicin da aka yi a watan Afrilu ya janyo artabu tsakanin 'yan sanda da kananan kabilu a yankin Uighur.

Lardin Xiajiang ya dade yana fuskantar tashin hankalin tsakanin 'yan kabilar Uighurs da kuma kabilar Han a kan batun shugabanci.

Karin bayani