Fursunonin Palasdinu sun isa gida

Fursunonin Palasdinu su ashirin da shida da Israila ta sako gabanin tattaunar zaman lafiya a Gabas ta tsakiya sun isa gabar yammacin kogin Jordan da zirin Gaza.

An wuce da goma sha daya daga cikin su zuwa gabar kogin Jordan, inda shugaba Mahmoud Abbas ya tarbesu.

Haka kuma yayinda suka fito daga gidan yari, jama'a da dama da suka halara a wurin sun rugumesu.

Isra'ila ta amince ta saki fursunonin ne sakamakon komawa kan teburin shawara gameda zaman lafiya a gabas ta tsakiya .

Sai dai wasu 'yan Israila sun nuna adawa game da matakin da gwamnatin kasar ta dauka.