Zanga-zangar ceto ilimi a Najeriya

Image caption Masu zanga-zanga

An gudanar da zanga-zanga a birnin Legas domin ceto bangaren ilimi a Najeriya wanda a yanzu ke cikin mawuyacin hali a kasar.

Wadanda suka shirya zanga-zangar sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zangar a fadin kasar, har sai mahukunta a Najeriya sun tashi tsaye wajen magance matsalolin da suka addabi bangaren ilimi.

Masu zanga-zangar ciki hadda kungiyar malaman jami'o'i data dalibai da kuma masu fafatukar kare hakkin bil'adama a Naijeriya sun ce babu gudu babu jada baya.

A cewarsu, a yanzu ilimi a Najeriya ya zama sai mai kudi, don gwamnati ta gaza wajen shawo kan matsalar.

A yanzu haka dai kusan watanni biyu kenan jami'o'i a Najeriya suna rufe sakamakon yajin aikin malamai.

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti da zai tattauna da malaman don warware matsalar.

Karin bayani