Birtaniya ta yi tur da kisan Konduga

Image caption Mark Simmond

Ministan ofishin kula da Afrika a ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya, ya yi tur da harin da aka kai a wani Masallaci a jihar Borno, lamarin daya janyo rasuwar mutane 44.

Mark Simmond ya ce maharan matsorata ne kuma kai hari a kan wajen ibada abune da ba za su laminta ba.

Ya kuma ce, gwamnatin Birtaniya tana za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin Najeriya a kokarin ta, na kawo karshen tashin hankalin da ake fuskanta a arewa maso gabashin kasar.

Shugabanni a Najeriya musamman 'yan siyasa su kuma sun shawarci jami'an tsaro su dukufa wajen magance matsalar kasancewar an kafa dokar ta-baci a yankin.

Sanata Ahmad Zanna dan majalisar dittajai daga jihar ta Borno, ya ce idan har jami'an tsaro suka baiwa fararen hula hadin kai, tabbas za a samu galaba wajen murkushe ayyukan 'yan bindiga.

Karin bayani