'Yan Taliban sun sace 'yar majalisa

'Yan kungiyar Taliban
Image caption Kungiyar Taliban na kai hare-hare a Afghanistan da Pakistan

A karon farko kungiyar Taliban ta sace wata 'yar majalisa, Fariba Ahmadi Kakar a Afghanistan.

A cewar 'yan sandan kasar an sace Fariba ne, a lokacin da take tafiya a lardin Ghazni dake tsakiyar kasar tare da 'ya'yanta mata uku.

An dai sako 'ya'yan nata daga bisani, kuma hakan na zuwa ne yayin da ake samun karuwar sace mata a kasar.

Taliban ta bukaci a sako wasu fursunonin kungiyar hudu, kafin ta saki 'yar majalisar.