ZTE ya yi waya mai manhajar 'Firefox'

Image caption Wayar ZTE wacce ta kafa tarihi

Kamfanin ZTE da ke kera wayar salula zai kasance kamfani na farko da zai sayar da wayoyin komai-da-ruwan-ka da ke kunshe da sabuwar manhajar Firefox a kasuwannin kasashen Birtaniya da Amurka.

A wani mataki da bai saba dauka ba, kamfanin zai sayar da wayar a kan kudi kusan fam 60, kuma za a sayar da ita ne a shagon ciniki ta hanyar intanet mai suna eBay.

Manhajar mai suna ZTE Open za ta rika amfani da hanyoyin sarrafawa na shafin intanet HTML5 maimakon wacce aka saba amfani da ita.

Shafin Mozilla, wanda shi ne ya kirkiri manhajar shiga intanet ta Firefox , ya ce wayar za ta samar da sababbin bangarori daban-daban na intanet.

Kakakin kamfanin China na ZTE ya ce za su mayar da hankali ne wajen sayar da wayoyin ga sababbin masu amfani da wayoyin komai-da-ruwan-ka.

Tuni dai kamfanin wayoyi na Telefonica ya fara sayar da wayoyin a Spain da Colombia da Venezuela.

Kamfanin ZTE ya ce nan ba da dadewa ba ne za a fara sayar da wayar a kamfanin sayar da wayoyi na eBay da ke Birtaniya da Amurka.

Karin bayani