''Yara 100,000 na fuskantar lalata''

Image caption A watan Mayu, hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanya an sako yara da dama da aka tilastawa shiga kungiyoyin masu dauke da makamai.

Kungiyar bayar da gaji ta Save the Children ta yi gargadin cewa fiye da yara 100,000 a kasar Afirka ta Tsakiya ke fuskantar yin lalata da su da sanya su cikin kungiyoyin masu dauke da makamai.

Kungiyar ta ce ana tursasawa yaran barin gidajensu tun bayan da gamayyar kungiyar 'yan tawaye ta kifar gwamnatin kasar a watan Maris.

A cewar kungiyar ta Save the Children, da dama daga cikin yaran suna fuskantar yunwa da cutar zazzabin cizon sauro.

Kakakin kungiyar, Mark Kaye, ya shaidawa BBC cewa an rusa kusan daukacin fannin kiwon lafiyar kasar.

Mista Michel Djotodia, wanda ya kwace iko daga Shugaba Francois Bozize lokacin da mayakan 'yan tawayen Seleka suka mamaye Bangui, babban birnin kasar ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2013, ya yi alkawarin mika mulki a hannun gwamnatin farar-hula a shekarar 2016.

A farkon watan da muke ciki, Sakatare Janar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya ce babu doka da oda a kasar tun da aka yi juyin mulki, kana fada ya kaure tsakanin manyan kungiyoyin 'yan tawaye guda biyu, lamarin da ya ta'azzara cin zarafin mutanen da ake yi.

'Mutane sun tsere daga gidajensu'

Kungiyar Save the Children ta ce iyalai da dama ba su da abincin da za su ci, kuma har yanzu da dama daga cikinsu suna boye a dazuka saboda suna tsoron dawowa cikin gari.

Image caption Sojojin kasashen duniya na kokarin dawo da kwanciyar hankali a kasar

Ta kara da cewa yaran da rigimar da ake yi a kasar ba ta shafa kai-tsaye ba sun ga yadda ake sace kayayyaki, sannan ana duka da kuma yi wa iyayensu barazanar kisa.

Mista Kaye ya ce satar da ake yi ba ta tsaya ga abinci da tufafi ba, har da magunguna.

A cewarsa, akwai bukatar kungiyoyin ba da agaji su kai dauki cikin gaggawa domin kaucewa aukuwar wani mummunan bala'i a kasar.

Karin bayani