'Afrika ta tsakiya na kawo barazanar tsaro'

'Yan tawayen jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Image caption 'Yara dubu 100 na fuskantar barazanar lalata a Afrika ta tsakiya, inji kungiyar agaji ta Save the children

Kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya ya yi gargadin cewa, jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na kawo barazana ga zaman lafiyar yankin.

Rashin bin doka da oda ya zama ruwan dare a cewara kwamitin.

Kwamitin ya nemi kungiyar tarayyar Afrika ta kara taimaka wa dakarun wanzar da zaman lafiya, kimanin dubu uku dake kasar.

Tun bayan korar shugaba Francois Bozize a watan Maris da 'yan tawaye suka yi, kasar ke fama da matsaloli kamar wawashe kayan jama'a da na gwamnati da cin zarfi ta hanyar fyade.

Kasar na da arzikin ma'adanan zinare da lu'ulu, amma tana fama da tashin hankali tun bayan samun 'yancin kai.