Chadi ta dakatar da kamfanin man China

Image caption Kamfanin tatar man Chadi

Gwamnatin Chadi ta ce, ta dakatar da dukan aikace-aikacen kamfanin mai na China a kasar, saboda ya janyo gurbatar muhalli.

Ministan man Chadin ya gaya wa BBC cewa, babban kamfanin man kasar Chinar da ke aiki a Chadin, ya janyo kwararar mai a wurare da dama, kusa da wani kurmi, inda yake aikin neman mai.

Ya bayyana barnar da cewa, babban laifi ne a kan muhalli, wanda ba za a amince da shi ba.

Tun shekara ta dubu biyu da tara ce, kamfanin man kasar Chinar ke gudanar da aikin neman mai a Chadin, kuma yana da matatar man a can.

Karin bayani