Ana zaman zulumi a Masar

Image caption Hazem El Beblawi ya kare matakin amfani da karfi domin tarwatsa masu zanga zanga

An shiga wata ranar ta zaman zulumi a kasar Masar bayan jami''an tsaro sun tilasta aiki da dokar hana yawon dare a birnin Alkahira da sauran wasu birane.

Alkaluman da hukuma ta bayar sun nuna mutane 280 aka kashe lokacinda aka tarwatsa taron masu boren a sansanoni 2 da suka kafa a birnin Alkahira da kuma a lokacin boren da ya biyo baya a sauran wasu biranen

Firayim ministan Masar na wucin gadi Hazem Beblawi ya kare matakin amfani da karfi domin tarwatsa sansanonin masu zanga-zanga a birnin Alkahira, inda ya ce hukumomi sun yi haka ne domin dawo da tsaro a cikin kasar.

Mr Beblawi ya ce sun wahala wajen yanke shawara a kan yadda zasu bulo wa lamarin.

Sai dai kungiyar 'yan uwa Musulmi ta ce mutane fiye da dubu 2 aka kashe a tashin hankalin.