Sojan da ya yi juyin mulki a Mali ya samu karin girma

Mali
Image caption Kyaftin Amadou Sanogo da ya jagoranci juyin mulkin soja a Mali a bara

Gwamnatin Mali ta karawa mutumin da ya jagoranci juyin mulkin soja a kasar girma daga kyaftin zuwa janarar.

Juyin mulkin a wancan lokaci ya jefa kasar cikin rudani.

Sai dai kungiyoyin kare hakin bil'adama sun yi Alla wadai da matakin karawa kyaftin Amadou Sanogo girma, a cewarta ya kamata a gudanar da bincike a kan rawar da ake zargin ya taka wajen azabtarwa da kuma wadanda suka bata a juyin mulkin soja da aka yi a watan maris din bara.

Juyin mulkin da sojoji suka yi , shi ne ya sa mayakan 'yan a ware na Abzinawa da masu kaifin kishin Islama suka kwace arewacin kasar ta Mali.

Haka kuma a bara aka yi wa shugabannin sojojin da suka yi juyin mulkin afuwa a wani mataki domin kawo karshen mulkin soja a kasar