An kafa gwamnatin hadin gwiwa a Nijar

Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou

Shugaban Nijar, Alhaji Mahamadou Isoufou ya sa hannu a kan wani kudurin yiwa gwamnatinsa garanbawul.

Wannan sabon kudurin da aka sanyawa hannu a ranar Talata, ya bada damar kafa gwamnatin hada kan kasa a Jamhuriyar ta Nijar.

Sababbin mambobin gwamnatin sun hada da wasu 'ya'yan jam'iyyar adawa ta MNSD Nasara, irin su Albade Abuba wanda aka nada a mukamin minista a fadar Shugaban Kasa.

Sauran sababbin ministocin sun hada da Wasalke Bukary da Malam Ada Shehu da Alhaji Alma Umaru.

Sai dai kuma kwamitin koli na jam'iyyar ta MNSD Nasara, ya ce ba da yawunsa za a shiga gwamnatin hada kan kasar ba.

Karin bayani