Masu kiba na iya fuskantar raunin kashi

Image caption Wani mai teba a cikin jirgin sama

Wani binciken kimiyya da aka gudanar a kasar Amurka ya nuna cewa mutane masu teba ko kuma kiba sosai sun fi fuskantar barazanar raunin kashi ko kuma rashin kwarin kashi da ake kira 'Osteoporosis', a turance.

Masana daga jami'ar Harvard wadanda suka yi nazarin, sun gudanar da gwaje-gwaje ne a kan mutane fiye da dari - maza da mata masu teba.

Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar Radiology ta Amurka, ya nuna cewa masu kiba sosai sun fi fuskantar hadarin raunin kashi da kuma zaizayewarsa, da ka iya haddasa saurin targade, ko karaya, ko kuma ciwon gabar kashi ko ma ciwon gabobi baki daya.

Binciken ya nuna cewa hatta a tsakanin masu kiba, mutanen da suka fi teba ta ciki ko kuma kwibinsu, sun fi nauyi da kuma kitse a cikin kashinsu; sun fi kasadar fuskantar cutar 'Osteoporosis' fiye da wadanda tebarsu ko kibar ta fi yawa ta manya-manyan cinyoyi da damatsa.

A kasashen Afirka da dama dai, kiba na daya daga cikin abubawan da mutane da dama ke dauka a matsayin alamomin jin dadi da kwanciyar hankali, amma ganin yadda bincike-binciken kimiya ke ci gaba da alakanta kiba da cututtuka da dama, masana cewa suke yi ya kyautu jama'a su fara sauya halayyarsu ta fuskar kiba ko kuma teba.