Amurka: Manning ya nemi afuwa

us Manning
Image caption Bradley Manning

Sojan Amurkanan da aka samu da laifin mika duban bayanan siri ga shafin wikileaks, ya yi magana a karon farko tun da aka soma yi masa sharia.

Bradley Manning ya fadawa kotun cewa ya yi nadama da abin da ya yiwa alummar kasar da ita kanta Amurka.

Ya ce a wancan lokaci be san cewa matakin da ya dauka na falasa bayannan siri abu ne da kan iya janyo illa.

An dai sami Private Manning da laifin leken asirin kasar, kuma zai fuskanci hukuncin daurin shekaru 90 a gidan yari.