'Zargin fyade a kan sojoji a Somalia'

Image caption Kwamanda a dakarun AMISOM

Rundunar tabbatar da tsaro ta kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somalia- AMISOM ta ce tana binciken zargin yin lalata da wata mata da ake yi wa sojojinta.

Matar ta ce an sace ta aka ba ta kwaya sannan aka yi ta mata fyade a farkon wannan watan.

A cewarta, dakarun Somalia da na AMISOM ne suka yi aika-aikar.

Lamarin ya janyo zanga-zanga daga wajen kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Mogadishu, babban birnin kasar.

Sojojin Somalia wadanda suka kunshi tsofaffin mayakan sa-kai, ana zarginsu da ta'asa, musamman batun yin lalata da mata.

Karin bayani