Bam ya hallaka mutane akalla sha hutu a Beirut

harin bam a Beirut
Image caption harin bam a Beirut

Wani bam ya tashi a kudancin Beruit, a yankin da galibi mazaunansa yan kungiyar Hezbolla ne.

Kafar yada labaran kasar ta bayyana cewa kimanin mutane sha hudu ne suka rasa rayukansu, yayinda wasu dari suka jikkata.

Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce bam din ya fashe ne tsakanin wasu gidaje biyu,inda ya lalata gine-gine da dama da kuma motoci.

Wannan shi ne karo na biyu da hakan ke faruwa cikin wata guda a kudancin Beirut, kuma wakilin BBC ya ce a bayyane take harin na da alaka da rikicin da ake yi a makwabciyar kasar, wato Syria, inda kungiyar Hezbolla ta nuna karara tana goyon bayan gwamnatin Bashar Al-Assad.