Brazil- Kotu ta sami wasu mutane da laifin fyade

Image caption Mutanen da ake zargin sun yi wata 'yar Amurka fyade

A kasar Brazil an yanke ma wasu mutane 2 hukuncin dauri na tsawon shekaru 49 a gidan Yari saboda sace da yin fyade ga wata mai yawon bude ido a Rio de Janeiro a cikin watan Maris.

Matar 'yar Amurka, direban wata Motar safa ne da yaron motar suka yi garkuwa da ita bayan ta hau motar a kusa da gabar teku dake Copacabana, suka kuma yi ma ta fyade a gaban

Saurayin ta wanda suka lakada wa dan karen-duka.

Lamarin dai ya ja hankalin jama'a ga batun kariyar lafiyarsu gabanin gasar wasannin kwallon kafa ta duniya da za a yi badi a kasar, da kuma gasar wasannin Olympics da za a yi a shekara ta dubu 2016.

Wani alkalin Kotu ya ce, dama gungun mutanen sun shafe watanni suna tafka abin asha a wannan yanki.