An kashe mutane fiye da 500 a Masar

Jana'izar wasu da suka mutu a tashin hanklin ranar Laraba
Image caption Kungiyar 'yan uwa Musulmi ta ce wadanda suka mutu sun fi 2,000

Gwamnatin Masar ta ce kimanin mutane 525 ne suka rasa rayukansu, a lokacin da dakarun soji suka tarwatsa sansanonin magoya bayan Mohammed Morsi.

Sai dai an yi amanna, yawan wadanda suka mutu sun haura hakan.

Mafi yawa daga cikin wadanda suka mutu an kashe su ne a birnin Alkahira, ko da yake an samu tashin hankali a wasu sassan kasar.

Laraba ta kasance ranar da aka yi matukar zubar da jini, tun lokacin da aka fara zanga-zanga a kasar shekaru biyu da suka wuce.