Amurka da Najeriya sun yi taro kan tsaro

Dakarun sojin Najeriya
Image caption Dakarun sojin Najeriya

Gwamnatin Amurka ta ce ya zama wajibi Najeriya ta kara kaimi ta fuskar tsaro, domin kare 'yan kasar daga abin da ta kira zubar da jinin da kungiyar Boko Haram ke yi.

Amurka ta kuma nemi Najeriyar ta kama tare da hukunta shugabannin kungiyar ta jama'atu Ahlus Sunna lil da'awati wal jihad.

Mataimakiyar Sakataren harkokin wajen Amurka ta fuskar siyasa, Wendy Sherman ce ta bayyana hakan a wajen wani taro kan sha'anin tsaro tsakanin Amurka da Najeriya a Abuja.

Amurkar ta ce dole Najeriya da sojojinta su nuna kauna ga al'umar arewacin kasar, tare da bada kariya da yin adalci ga wadanda tashin hankalin kungiyar ta shafa.

Babban sakataren ma'aikatar harkokin wajen Najeriya jakada Martin Uhomobihi, yace gwamnatin kasarsa ta tanadi kudade da ma'aikata masu dimbin yawa domin shawo kan matsalar.