Masar ta yi wa Obama raddi

Ginin da aka sanya wa wuta a Giza
Image caption An samu arangama tsakanin 'yan uwa musulmi da mazauna wajen birnin Alexandria

Fadar Shugaban kasar Masar ta ce takaicin da Shugaba Obama ya nuna a kan matakin da aka dauka a kan magoya bayan kungiyar 'yan uwa Musulmi zai kara karfafa gwiwar kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.

A cikin wata sanarwa, Fadar Shugaban kasar ta ce, Kasar tana fuskantar abin da ta kira hare-haren 'yan ta'adda.

A ranar Alhamis, Mr Obama ya ce, hadin kan da Amurka ke da shi da kasar Masar ba zai ci gaba ba kamar yadda yake a da, a yayin da ake kisan farar hula a kan tituna.

Haka kuma kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani zaman gaggawa a kan lamarin kuma ya nuna takaici game da rayukan da aka rasa, tare da yin kira ga dukkan bangarorin su daure, su mayar da wukakensu a kube.

Kungiyar 'yan uwa Musulmi ta yi kira da a yi tarukkan gangami na zanga-zanga bayan sallar Jumma'a yau a birnin Alkahira a kan abin da ta kira "ranar nuna bacin-rai".