An kirkiri manhajar waya ta tiyatar ido

Manhajar wayar komai da ruwanka da ake tiyatar yanar ido da ita
Image caption Manhajar wayar komai da ruwanka da ake tiyatar yanar ido da ita

Masana ilimin kimiyya a Birtaniya sun kirkiro wata manhajar wayar komai da ruwanka, da za ta kawo gagarumin sauyi a bangaren kula da idanu a kasashe masu tasowa.

Manhajar za ta baiwa ma'aikatan lafiya damar duba wa ko akwai cuta a ido, kuma su yi gwaji da na'ura 'yar karama mafi araha.

Image caption Manhajar waya ta tiyatar yanar gizo

Akasarin wadanda ke fama da matsalar ido a kasashe masu tasowa na yankunan karkara, inda likitocin idanun da za su taimaka musu ba sa iya zuwa.

Mutane fiye da miliyan 285 ne a fadin duniya, ke fama da matsalar gani ko kuma makanta.

Ana tunanin cewa za a iya rigakafi ko magance hudu zuwa biyar na matsalolin ido, ta hanyar yin tiyatar yanar ido mai sauki, ko kuma ma amfani da tabarau.

A yanzu haka ana kan gwajin wannan manhaja a kan mutane 5000 a wasu kauyuka na kasar Kenya.

Karin bayani