Barkewar cutar shan-inna a Somalia

Image caption Riga-kafin cutar Polio

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa cutar shan-inna da ta barke na yaduwa a kasar Somalia.

Ofishin Majalisar dinkin duniya dake kula da ayyukan jin kai ya ce an tabbatar da akalla yara 105 na fama da cutar.

A cewar ofishin, an yi wa kusan yara miliyon hudu allurar riga kafi sannan an kaiwa yara fiye da dubu dari shida magani a kudanci da tsakiyar Somalia-wato yankunan da kungiyar Al Shabab ke da karfi.

Gargadin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da kungiyar agaji ta MSF ta sanar da dakatar da ayyukanta a Somalia.

Kungiyar MSF na da ma'aikata kusan 1,500 wadanda suke yin ayyuka daban-daban a cikin Somalia.

Karin bayani