Bikin tunawa da ma'aikatan Marikana

South africa
Image caption Dangin ma'aikatan da suka rasu

Idan an jima a yau ne za a gudanarda bikin cika shekara daya da kisan da 'yan sanda suka yi ma ma'aikata 34 na mahakar ma'adinai dake yajin aiki a Marikana.

Ana sa ran, Matan wadanda aka kashe da mutanen da suka samu raunuka a lokacinda 'yan sandan suka bude ma ma'aikatan wuta da kuma dubban ma'aikatan ma'adinan za su hallara a wurinda lamarin ya faru a bara.

Kisan ma'aikatan a lokacinda suke boren neman karin albashi ya girgiza kasar Afrika ta Kudun.

Ya kuma yi matukar illa ga tabbacin da ake da shi na muhimmancin da kasar ta baiwa masana'antar hakar ma'adinai.