Za a tura masu binciken makamai Syria

'Yan tawayen Syria
Image caption Miliyoyin 'yan Syria ne suka tsere zuwa makotan kasashe, saboda rikici tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana gab da tura tawagar masu binciken makamai kasar Syria.

Wani kakaki ya ce gwamnatin Syria ta amince tawagar ta kasance a kasar har tsawon mako biyu.

Makonni biyu da suka wuce ne Majalisar ta ce, gwamnatin Syria ta amince bisa fahimta cewa za ta bar masu binciken su je gurare uku da ake zargin anyi amfani da makamai masu guba.

Guraren sun hada da kusa da Aleppo, inda gwamnatin ta yi zargin cewa 'yan tawaye sun yi amfani da makamai masu guba wajen kashe mutane 26 a watan Maris.