Ana satar gashin mata a Venezuela

Image caption Wasu 'yan Afrika na kawa da gashi

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya yi kira ga 'yan sandan kasar, su dauki mataki a kan gungun mutanen dake satar gashin mata.

A wasu lokutan barayin kan ritsa mata da bindiga, su kuma sa matan tufke gashin guri guda, kafin su yanke.

Suna sayar da gashin ne a guraren gyaran gashi na mata.

Kuma ana amfani da shi wajen karin gashi ko kuma a yi hular gashi.

Matsalar satar gashin na karuwa, musamman a birni na biyu mafi girma, Maracaibo a cewar kafafen yada labarai na cikin gida.