China za ta daina amfani da sassan jikin fursunoni

Image caption China ta sha musanta cewa tana amfani da sassan jikin fursunoni

Kasar China ta ce daga watan Nuwamba za ta daina amfani da sassan jikin mutanen da aka yankewa hukuncin kisa domin dasawa mutanen da ba su da lafiya.

Shugaban sashen da ke kula da dashen sassan jikin mutane na kasar, Huang Jiefu ne ya bayyana hakan.

A halin da ake ciki, jami'an lafiyar kasar suna yin wani shiri da suke fatan zai sa mutane su bayar da kyautar wani sashen jikinsu, wadanda a baya ba sa son bayarwa saboda al'adarsu ta hana binne mutane ba tare da wani sashe na jikinsu ba.

A shekaru da dama kasar China ta musanta cewa tana amfani da sassan jikin fursunonin da aka yankewa hukuncin kisa, sai dai a 'yan shekarun baya-bayan nan ta amince cewa tana daukar wannan mataki.

Karin bayani