An ceto yara fiye da 80 a Congo

Congo
Image caption Wani yaro dake rike da bindiga

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun ce sun ceto yara fiye da 80, wasun su ma 'yan kimanin shekaru 8 da haihuwa daga gungun mahara da suka sace su.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce yaran wadanda suka hada da 'yan Mata 13, sojin sa kai ne na Mai-Mai suka tilasta musu shiga gwagwarmaya da makamai a cikin watanni 6 da suka gabata.

Sojin sa kan na Mai-Mai dai suna gudanar da harkokinsu ne a lardin Katanga na Kudu maso gabashin kasar.

Wakilin BBC ya ce, ana dauki-ba dadi a yankin, saboda sojin sa kai na yankin suna gwagwarmayar neman sai lallai an yi adalci wajen rabon arzikin ma'adinai da ake hakowa a kudancin kasar.

An hada 40 daga cikin yaran da 'yan uwansu, a yayinda sauran ake duba lafiyarsu.