'Yan bindiga sun kai wa Damboa hari

Borno maiduguri
Image caption Gwamnan jihar Borno Alhaji Shettima Kassim

Wasu 'yan bindiga sun kai wa garin Dambao hari dake jihar Borno abin da ya yi sandiyyar mutuwar mutane goma sha daya.

Rahotani sun ce wadanda suka shaida lamarin sun ce yan bindigar sun budewa farar hula da 'yan sanda wuta a garin na Damboa mai nisan kilomita 85 da Maiduguri.

Sai dai sun ce jamian tsaro sun sha karfin 'yan bindigar da suka kai wa wani ofishin 'yan sanda da wurin bincike na sojoji hari.

Kawo yanzu ba'a san ko su wanene ba su kai harin amma yanki ne da kungiyar da ake kira boko haram ke tasiri sosai.

A yanzu ne bayanai suka soma fitowa game da lamarin saboda katsewar layukan sadarwa da sojoji suka yi a jihar ta Borno tun a watan Mayun daya gabata a lokacin da aka kafa dokar ta baci.