Jami'an tsaro a Masar sun shiga wani Masallaci

Masar
Image caption Rikicin Masar

Jami'an tsaro a kasar Masar sun shiga wani Masallaci dake birnin Alkahira wurin da daruruwan magoya bayan kungiyar 'yan uwa Musulmi suka fake da daren jiya.

Alamu na nuni da cewa sojojin suna kokarin sasantawa ne da masu boren don lallashinsu su fice daga cikin masallacin na al-Fateh.

Wakilin BBC a birnin Alhakira ya ce ga alama wasu mutanen sun yarda, amma har yanzu akwai wasu masu yawa dake cikin masallacin.

Hukumomi sun ce mutane fiye da 80 aka kashe a arrangamar da magoya bayan hambararren shugaban Masar, Muhammed Mursi suka yi da jami'an tsaro jiya juma'a

A jiya ne Jam'iyyar ta 'yan uwa musulmi ta umarci jama'a su fito domin nuna bakin cikinsu game da tartsawar da jami'an tsaro suka yi wa mutane daga sansanonin da suka kafa a Alkahira ranar Laraba, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.

Karin bayani