An kashe mutane sama da 170 a Masar.

Hukumomin kasar Masar sun ce mutane fiye da dari da saba'in ne aka kashe, tare da raunata dubu da dari biyu a taho-mu-gamar da aka yi cikin sa'o'i ashirin da hudun da suka wuce a kasar.

An kama 'yan kungiyar Ikhwanul Musulmin wato 'Yan'uwa Musulmi su fiye da dubu daya, cikinsu har da dan'uwan jagoran kungiyar Alka'ida, Ayman al-Zawahiri. Wani kakakin gwamnati, Sherif Shawki - ya ce Firaministan Hazem

Beblawi, yana tunanin haramta kungiyar ta Ikhwan.