Jami'an Masar sun ce sun fitar da 'yan Uwa Musulmi daga masallacin Al-Fateh

Wani magoyin bayan Mursi
Image caption Wani magoyin bayan Mursi

Dakarun tsaro a Masar sun ce sun fitar da dukkan mutanen da suke cikin masallacin Al-Fathi dake birnin Alkahira, inda magoya bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi suka nemi mafaka. Jan dagar a masallacin na Fathi ya dauki sa'o'i da dama, inda shaidu suka bayyana ganin amfani da bindigogi da barkonon tsohuwa.

Lokacin da soji ke ci gaba da yin kawanya ga masallacin, hotunan talabijin sun nuna jami'an tsaro suna zuwa ga hasumiyar masallacin.

Jiya da dare, soji sun shiga masallacin su nemi mutane su fita, wadanda suka fitan an rika dukansu - hakan ya sa saura suka ji tsoron ficewa.