Kotu ta soke tuhumar kage kan wani malami a Pakistan

Malam Khalid Jadoon
Image caption Malam Khalid Jadoon

Kotu a Pakistan ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa Malamin Islaman ne da aka kama bisa zargin yin kage a kan wata yarinya Kirista da aka zarga da yin sabo.

Yarinyar, Rimsha Masih, an tsare ta a kurkuku tsawon makonni bayan da Khalid Jadoon ya zarge ta da kona wasu shafuka na Alkur'ani Mai Tsarki.

Wasu ne suka ce sun gan shi yana sanya wasu shafuka na Alkur'anin a cikin jakar yarinyar.

An janye tuhumar ne bayan da wadanda suka ba da sheda a kansa suka janye shedar da suka bayar.

Batun ya jawo damuwa game da amfani da dokar Pakistan din a kan sabo, wadda ke da karfin gaske.