Al-Sisi ya gargadi masu goyan bayan Morsi

Abdel Fatah Al-Sisi
Image caption An tsare daruruwan magoya bayan Mr. Morsi

Shugaban rundunar sojin kasa a Masar Abdel Fattah al-Sisi ya yiwa magoya bayan hanbararren Shugaban Masar Mohammed Morsi gargadin cewar ba za a lamunce da duk wani tashin hankali ba.

Amma a wani jawabi da yayi ga sojoji da 'yan sanda, ya ce akwai dama ga kowa a Kasar.

Wadannan sune kalamai na farko da yayi tun lokacin da dakarun tsaro suka dauki mataki akan 'yan jam'iyyar 'yan uwa musulmi tasu Mr Morsi, al'amrin da yai sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Kungiyar dai ta soke wani gangami data tsara yi a birnin Alkahira a yau.

An dai tsare magoya bayan kungiyar da dama a daukacin Kasar.

An kuma gabatar da shawarar rushe kungiyar Islamar wanda za a tattauna batun a taron majalisar ministocin Kasar.

Karin bayani