Majalisar gudanarwar Masar za ta yi wani zama

Rikicin kasar Masar
Image caption Rikicin kasar Masar

Majalisar gudanarwar Masar za ta yi wani zama, yayin da rikici tsakanin dakarun gwamnati da magoya bayan hambararren shugaba Morsi ke kara ta'azzara.

Fira Ministan rikon kwarya, Hazem el-Bablawi na tunanin rushe kungiyar ta 'Yan uwa Musulmi, wacce Mr Morsi memba ne a ciki.

Mr Beblawi ya ce babu wani zancen sasantawa da mutanen da ke da hannu wajen zub da jini.

A jiya Asabar ne jami'an tsaro suka fatattaki mutanen da ke cikin masallacin Al-Fateh a birnin Alkahira, inda magoya bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi suka kafa shingaye.

Jan dagar ya dau tsawon sa'o'i da dama, da shedu suka bayyana ganin amfani da bindigogi da hayaki mai sa hawaye.

Jami'an tsaron na cewa sun cafke mutane da dama, ciki har da 'yan kasashen waje.

Kana ana bincikar kimanin 250 daga cikinsu da ake zargi da aikata laifukan da suka kisan kai da ta'addanci.

Askandariya

Masu zanga-zanga sun fito kan tituna a birane da dama na Masar, inda suka yi biris da dokar hana fitar dare da gwamnatin da ke da goyon bayan soji suka kafa tun ranar Laraba.

Hotunan talabijin sun nuna masu zanga-zanga a birni na biyu a girma a Masar, Askandariya da kuma Helwan da Minya da ke kudancin birnin Alkahira.

Ana iyan ganin tankokin yaki a kusa da hanyar gabar teku dake birnin Askandariya.

Amma duk da haka babu wasu rahotanni da suka bayyana barkewar wasu sabbin tashe-tashen hankula.

Tankokin yakin da aka girke a wurare daban-daban na nufin tilasta dokar hana fitar dare.

A baya bayan nan dai gwamnatin rikon kwaryar kasar ta ce tana tunanin daukar matakin rushe kungiyar 'yan Uwa Musulmi.

Wani kakakin gwamnatin ya shaidawa manema labarai birnin Alkahira cewa dawowar 'yan kngiyar masu tsattauran ra'ayin addinin Islamar ba mai yiwuwa ba ne.

A birnin Alkahirar, ana sa ran bude bankuna bayan da aka rufe tun ranar Laraba, kana za a fara gudanar da hada-hadar hannayen jari da suma suka tsaya cik a kasar.